Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - An kai gawar marigayi ne a cocin St George's Cathedral da ke Cape Town a a wannan Alhamis inda za ta kwashe kwana biyu domin mutane su yi ban kwana da ita.
A hukumance za a yi jana'izarsa ranar Asabar 1 ga watan Janairu bayan mutane sun gama ban kwana da gawarsa, sannan za a kona gawarsa a kuma ajiye tokar a cikin cocin, inda ya kwashe shekaru da dama yana wa'azi.
Desmond Tutu wanda ake matukar mutuntawa, wanda ya kasance a sawun gaba wajen yaki da gwamnatin wariyar launin fata, ya taba samun lambar yabo ta nobel kan zaman lafiya.
342/